XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da Mallam Ibrahim Zakzaky na goma sha daya

Sayyed Zakzaky2

Ko ya halasta mutum ya dauki dan siyasa a mashin su tafi kamfe (Achaba)?
TAMBAYA: Akramakalla. Duk lokacin da nake salla sa hutu ya rika zuwa mani amma sai in rika matsawa sai wasiwasi ya rika zuwa mani. To yaya zan yi?

Daga Nasiru bauchi Yelwa S/K

SHAIKH ZAKZAKY: Akwai haddin da zai zama salla ta baci. Amma idan dai har mutum ya ji, ya rike, ya zama bai hana dumanina ba (abin da ake ce ma dumanina, natsuwa a salla ba), ya zama shi kenan sai abin ya koma bai fito ba, shi kenan zance ya kare ba wani abu. Amma da zai zama suna ta kokawa da shi, har ya rasa natsuwa, to salla ta baci, saboda natsuwa salla wajibi ne.


TAMBAYA: Akramakallah. Na dauki ruwan da abokina ya ajiye na yi alwala da shi, amma ba ya nan, amma ina da tabbacin cewa in yana nan ba zai hana ni ba. Yaya matsayin sallata?

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai wannan ba komai saboda shi abin da al'ada ta riga ta gudana kan cewa ana iya amfani da shi na ruwa, shi kenan ba komai, ko da ba da izinin mai ruwan ne ba, in dai ka san al'adar mutane an saba irin wannan, in an ga ruwa haka nan ana iya amfani da shi.

TAMBAYA: Allah ya ji kan Malam, ana cewa fita jihadi sai da yardar iyaye, kuma idan mutum ya je ba da yardarsu ba aka kashe shi, bai yi shahada ba. Ya abin yake?

Daga Nasiru Bauchi Yelwa S/K

SHAIKH ZAKZAKY: Cewar bai yi shahada ba, lallai ban san wannan ba. Saboda shi izinin iyaye ga yaro karami wanda bai balaga ba, hakki ne na iyaye din, amma ba a ce in ya je ya yi shahada kuma shi ba shahidi ne ba! Sai dai hakkinsu ne yaro, karami, wanda bai balaga ba shi ma ake nufi, ya nemi izini. Ba a ce baligi, magidanci shi ma sai ya nemi izinin iyayensa ba. Saboda haka hakkinsu ne ga yaro karami ya nemi izininsu. Haka ma yanzu wannan jihadin kila yana fadin abin da yake kila karantawa kawai, to hatta ma kamar azumin nafila misali, ko wadansu ayyuka irin wadannan na nafila, shi ma sai da izinin iyaye. Amma ba a ce in ya yi ba da izinininsu ba, ba shi da lada ba. Ba a ce haka nan ba, sai dai hakkinsu ne, ya kuma kamata ya ba su.

TAMBAYA: Akramakallah, menene hukuncin a mayar da bunsuru taure ta hanyar dandaka?

Daga Abdulkadir Zakariyya unguwar Dahiru Funtuwa.

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai malamai sun nuna cewa in dai don gyaran nama ne kuma bai cutar da shi bunsurun ba, shi kenan. Akwai fidiya akwai dandaka. Na'am tana iya yiwuwa daidai lokacin da ake yin bunsurun ya dan ji wahala, to amma daga baya shi kenan zai yi nasa sha'ani, tunda dai bunsuru ne, babu laifi. Amma ga mutum namiji bawa, shi wannan haramun ne, wanda har yanzu abin mamaki a wadansu wurare ana yi. Sai a ce wannan bawa ne sai a dandake shi, a sa shi ya shiga cikin mata yana masu hidima. To wannan kam ya haramta.

TAMBAYA: Assalamu alaikum Malam. Na yi alwala sai na ci garo, ina cikin salla sai na ji shi a bakina har na dan hadiye, ya matsayin sallata?

Daga Abubakar Ali Likoro, Muciya Sabon gari Zariya.

SHAIKH ZAKZAKY: To babu laifi ga wani dan abin da ba a ka rasa ba, wanda ya dan kude ma mutum a baki, ba da shi ya ji shi ya yadiye shi da unwanin yana ci ba. Amma da da ya ji dan kulun goro din, ya dan ji ashe dan ragowar goro ne, sai ya dan tauna da gangan, to za mu za mu ce ya ci goro. Amma idan dai kawai haka nan sai ya ji dan miyau ko ya hadiye, to ba sunansa ci bane. Ma'ana ci da sha su suka haramta a salla. Amma idan wani abu ya shige bakin mutum ba da unwanin ya ci ko ya sha ba, to ba zai zama ya bata masa salla ba. Saboda haka muna iya cewa in dan guggubin ya ji shi ya yi ta'ammudin taunawa musamman da nufin yana cin goro, sai a ce ya ci goro. Amma in don wani dan bangare ya dan fada masa a baki tare da miyau, wannan ba komai.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ko zan iya in bi jam'in salla a bayyane, alhali ina nufin salla ni kadai?

Daga Abubakar Ali Likoro, Muciya Sabon gari Zariya.

SHAIKH ZAKZAKY: Eh ya halatta. Kuma kana iya ruku'u da sujada tare da Liman alhali kai da unwanin kai kadai kake salla. Kuma ma kana iya bin Liman a wani wuri a wani bangare na sallar kuma ka koma kana yi kai kadai a wani bangare, wato kamar dama can ka fara bin shi daga wani lokacin, kuma sai ka yanke shawarar ka fasa bi, yanzu ka zama mai sallarka.

TAMBAYA: Akramakallah, ko ya halasta mutum ya dauki dan siyasa a mashin su tafi kamfe a matsayin haya? Daga Abubakar Ali Likoro, Muciya Sabon gari Zariya.

SHAIKH ZAKZAKY: To, shi dai da a ce misali zai dauki mutum ya kai shi wani wuri ne shi kenan, daga nan sai ya biya shi ladansa, to sai mu ce wannan babu laifi da shi. Amma idan msiali in zai shiga kwararon kamfen din ne ana fantsan-fantsan a manna wa mashin din Fosta, shi kuma a rika cewa sai wane! To lallai yana kamfe ne. Kuma abin da ya same shi a tafarkin wannan kamfe din dai yana daidai da abin da ya shafi wadancan. Alal misali kila ma ya yi shahada a wannan kamfe din. Alal misali ya dauke su ne suka lika fosta din suna kamfe din su, tana iya yiwuwa 'yan adawa su far masu. To ka ga a nan ma tana iya yiwuwa wa ya yi shahada a wannan kamfen, ka ga ya yi shahadar siyasa kenan ko? Saboda haka ya danganta da yadda al'amarin yake ne. Amma in misali wannan dan siyasa ne (ya ce) ka dauke ni ka kai ni wuri kaza, kuma wurin nan za ka je ka sauke shi ne, shi kuma can za shi kamfe ne, ka ga ai wannan kai bai shafe ka ba, za ka iya yi. Kai ba kamfen kake yi ba. Amma yanzu ka dauke shi ku bi titi yana wakar jam'iyyarsa, ana haya-haya, ana yabo, ana zagi, har ma a harbo dutse, to ke ga kana cikin kamfe. Saboda haka makomarka makomarsa kenan.

TAMBAYA: An ce mace ba ta bayyana karatu a wajen da ake bayyanawa. To idan ta manta ta bayyana, yaya sallarta?

Daga Haladu Audu Asibitin Yadi buni, jihar Yobe.

SHAIKH ZAKZAKY: To tana iya bayyanawa. An hana ta bayyanawa ga jin wani ajnabi ne. Idan a dakinta take sallah, ba wanda zai ji, sai mijinta, sai muharramanta, ta samu ta bayyana muryarta. An hana bayyana muryar ga wani ne na waje, ba bayyana muryar ne kawai aka hana ba. Saboda haka ba da mantuwa ba, ko da gangan ne, tana iya yi, idan dai wani ba zai ji ba. Amma idan mantuwar ya sa ta manta ta yi, kuma wani ajnabi ya ji, to wannan bai bata sallarta ba. Sai dai abin da ta yi tunda mantuwa ne, to ba komai. Da gangan ne ba za ta yi ba.

TAMBAYA: Mutum zai iya canza taklidi daga Mai risala zuwa Mujtahidi?

Daga Muhammad Mansur Usman Bature Bauchi.

SHAIKH ZAKZAKY: To ni ban san ma'anar Mai risala ba. Domin abin da muka sani (shi ne) ana yin taklidi da Mujtahidi ne, shi Mujtahidi ne yake rubuta Risala. Risala kamar sako ne na hukunce-hukuncen da shi Mujtahidin ya rubuta. (Saboda a nan kamar abin da ya nuna kamar Mujtahidi daban, Mai risala daban. Da ma abin da yake tambaya shi ne mutum yana iya canza taklidi daga Risalar wani Mujtahidi zuwa Risalar wani Mujtahidi, wanda yake nufin kawai daga Mujtahidi zuwa wani Mujtahidi, tambayan kenan). Sai mu ce masa, in haka nan ne daga Mujtahidi zuwa Mujtahidi yake nufi, sai mu ce eh! Amma kalmar Mai Risala, lallai ba ta da wani ma'ana a nan, don Mujtahidai ne ke rubuta Risala, kuma ba masu Risala ake ce masu ba.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din